Kafafen watsa labarun HKI sun ce, Amurka ta bayyana cewa, MDD ta ki aiki tare da kamfanonin Amurka da na Isra’ila domin raba kayan agaji a Gaza.
Majiyar ta HKI ta kuma kara da cewa; An jinkirta aiwatar da Shirin na raba kayan agajin saboda wasu dalilai na kayan aiki.
Wuraren hudu ne dai aka ware domin raba kayan agajin a kudancin Gaza, an kuma kai shi zuwa mako na gaba.
Wasu kafofin watsa labaru sun ambato babban magatakardar MDD yana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani shiri a Gaza wanda ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba.
A cikin wani bayani da wata kungiya mai kula da iyalai a yankin Gaza ta fitar, ta nuna kin amincewarta da tsallake kungiyoyin kasa da kasa a wajen raba kayan agajin.
Ana zargin Amurka da HKI da kokarin tattara bayanai akan fuskoki, idanu da kuma DNA na iyalan da za a bai wa tallafin abinci, da hakan zai bayar da damar cutar da Falasdinawan Gaza da kuma kashe wanda suke so a nan gaba.