Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Sami Nasara Ne Tare Da Goyon Bayan Mutane

Ministan gina tituna da raya birane na kasar Iran ta bayyana cewa juyin juya halin musulunci a kasar Iran ya sami nasara a kasar Iran

Ministan gina tituna da raya birane na kasar Iran ta bayyana cewa juyin juya halin musulunci a kasar Iran ya sami nasara a kasar Iran a shekara ta 1979 ne tare da goyon bayan mutane, sannan har yanzun masana basu kammala bincike don sanin irin karfin tasirin da wannan juyin juya halin yayi a cikin kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya a bangaririn siyasa tattalin arziki zamantakewa da sauransu ba.

Malaman Farzaneh Sadegh  ta bayyana haka ne a jawabin da ta gabatar a karamin ofishin jakadancin JMI dake birnin Istambul na kasar Turkiya a iya alhamis.

A jiya alhamis ne karamin offishin jakadancin JMI ta gudanar da taro da bikin cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halain musulunci a kasar Iran inda ya gayyaci ministan a matsayin babbar bakuwa mai jawabi a taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted