JMI Ta Bayyana Cewa Jami’an Tsaron Kan Iyakar Kasar Sun Fatattaki Wasu Yan Ta’adda A Kudu Maso Gabacin Kasar

Babban kwamandan jami’an tsaro wadanda suke kula da kan iyakokin kasar Iran daga kudu maso gabacin kasar sun sami damar wargaza wata tawagar yan ta’adda

Babban kwamandan jami’an tsaro wadanda suke kula da kan iyakokin kasar Iran daga kudu maso gabacin kasar sun sami damar wargaza wata tawagar yan ta’adda wadanda suke kokarin kutsawa cikin kasar don aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto babban kwamandan jami’an tsaro na kan iyaka a lardin Sistan Baluchestan Burgedia Janar Ahmad Ali Goudarzi yana fadar haka a yau Asabar.

Goudarzi ya kara da cewa saboda sanya ido da kuma aiki dare da rana a kan iyakokin kasar Iran da Pakistan, jami’an tsaron kasar sun farwa yan ta’adda a garin sirkan bayan sun shiga kasar a darejn jiya jumma’a, kuma an yi musayar wuta da su, har kuma aka kashe 2 daga cikinsu. Banda haka Goudarzi ya ce sun kwace makamai masu yawa a hannunsu, da kuma wasu kayakin aikin soje wadanda suka hada da Magazin 21, chajan wuta na wayoyi guda biyu, wata na’uran daukan hotuna nau’in infrated, da bom guda daya da batiran boma bomai guda biyu, da wayar hannu guda daya da kuma wayar hannu mai amfani da satellite. Sai kuma sauran kayakin sawa da abinci da sauransu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments