Jiragen saman yakin kawancen Amurka masu yaki da abinda suka kira ta’addanci sun keta hurumin sararin samaniyar kasar Siriya har sau 14 a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin shugaban cibiyar sasanta yan siriya na kasar Rasha da ke birnin birnin Damascus na kasar Siriya, Oleg Ignusyuk yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa jiragen yakin kawancen sun hada da samfurin F-15 guda 3, sai samfurin Typhoon guda biyu sannan sannan wasu samfurin A-10 guda uku. Jiragen yakin sun ratsa ta yankin Al-Tanf na kasar ta siriya inji Oleg.
Shawagin wadan jiragen yaki suka dai yana rikita zirga zirgan jiragen fasinja a yankin. Banda haka suna samar da matsaloli a harkar zirga zirgar jiragen saman Fasinja a yankin.
Yankin Al-Tanf dai, yanki ne mai matukar muhimmanci a kasar ta Siriya, don yana kan iyaka da kasashen Jordan da Iraki. Gwamnatin Amurka ta samar da sansanin sojojintac a yankin don kula da abubuwan da ke faruwa a cikin kasashen guda 3, da kuma sanya ido a kan kayakin da suke wucewa daga Iran zuwa cikin kasar Siriya.