Tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad na kasar Siriya ne, sojojin HKI suka fara kai hare-haren don lalata makaman kasar ta Siriya a wurare daban daban a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bada labarin cewa, a jiya Asabar ma, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan rumbunan ajiyar makamai a birnin Lantakia na kasar ta Sirya.
Mazauna yankin sun bayyana cewa sun ji karar fashe-fashe makamai a gewajen garin, sannan kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha suma sun tabbatar da cewa an ji karar fashe-fashe a birnin, kuma jiragen yakin HKI ne suka kai hare hare.
Har yanzun babu labarin irin asarorin da aka yi sanadiyyar hare-haren na HKI a Lantakia.