Jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun cilla makamai kan Falasdinawa 5 wadanda suke jiran karban abinci a wata cibiyar raba abinci wacce ake kira ‘Community Kitchen’ a sansanin yan gudun hijira na Narairat a tsakiyar Gaza a safiyar yau Laraba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, 4 daga cikin mutanen da yahudawan suka kaisu ga shahada yara kanana ne, wadanda suka zo karabawwa iyalansu abinci a cibiyar.
Labarin ya kara da cewa an kai gawakin mutanen biyar asbitan Awda dake garin Jabalia, wanda yafi kusa da sansanin yan gudun hijiran.
Hukumar bada agaji ta MDD, UNRWA ta bada labarin cewa, saboda kofar ragon da HKI take wa Falasdinawa a Gaza, mafi yawansu sun dogara da abincin agaji ne don rayuwa.
Unurwa Ta kara da cewa iyalai da dama a zirin gaza suna kwana da yunwa saboda rashin abinci, da kuma hana shigo da kome wanda gwamnatin HKI take yi wa yankin fiye da shekara guda.
Labarin ya kammala da cewa wannan ba shi ne karon farko wanda jiragen yakin HKI suke kashe falasdinawa suna layin karban abinci ba.
A tsakiyar Gaza dai sojojin yahudawan sun rusa gine-gine kimani 600 saboda kafa sansanin sojojinsu a wurin.