Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Sabbin Hare Hare Kan Yakuna 4 A Kasar Yamen

A cikin sabban hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Alhamis sun kai hare-hare kan larduna guda 4 . Tashar

A cikin sabban hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Alhamis sun kai hare-hare kan larduna guda 4 .

Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ta nakalto majiyar labarai daga kasar ta Yemen jiragen yakin Amurka suna kai hare-haren a kan kasar kusan ko wani rana.

Amurka dai tace tana kai wadan nan hare-hare kan kasar Yemen ne sai ta dakadar da kaiwa HKI hare-hare don goyon bayan Falasdinawa a Gaza, sannan ta dakatar da kaiwa Jiragen HKI da kuma na Amurka hare-hare a cikin tekun maliya.

Kamfanin dillancin labaran SABA NEWS na kasar Yemen ya nakalto wani jami’an gwamnatin kasar wanda bai son a bayyana sunansa yana cewa jiragen yakin Amurka sun kai hare hare a safiyar yau Jumma’a a tsibirin Kamaran da ke kudancin kasar kusa ba bakin tekn red sea.

Sannan makaman na Amurka sun fada kan yankin Bani Hushaysh da ke daya daga cikin lardunan da suke kusa da San’aa babban birnin kasar.

Labaran sun kara da cewa makaman Amurka sun fada kan garin Hakamal-Haymah da yankin Manakhah duk a kusa da birnin san’aa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments