Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda a nan take suka kashe falasdinawa kimani 30 sannan wasu da dama suka ji rauni.
Sai kuma a kan sansanin yan gudun hijira na Nusairat jiragen yakin HKI sun kashe muatne akalla 8 wanda ya kawo jimillar wadanda aka kashe zuwa lokacin bada wannan labarin zuwa 38. Wasu da dama sun ji rauni. Raunukan wasu yana da hatsari mai yuwa yam utu nan gaba.
Sannan majiyar sojojin HKI ta bayyana cewa zuwa lokacin bada wannan labaran sun kai hare-hare har gusa 45 a kan yankuna daban daban a gaza.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 dai zuwa yanzo sojojin yahudawan HKI sun kashe Falasdinawa akalla dubu 51.a yayinda wasu fiye da dubu 100 sun ji rauni.