Jeremy Corbyn  Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai  Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa

Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta

Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan  ranar 7 ga watan Okotoba 2023.

Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa;  A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa.

Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.”

A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai na biliyoyin Fam, kuma da akwai rahotanni da suke nuni da cewa an yi amfani da su a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar Falasdinawa.

Tun farkon yakin Gaza a watan Oktoba 2023, al’ummar kasar Birtaniya ta kasance a gaba-gaba wajen gudanar da Zanga-zangar yin tir da HKI da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments