Babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Imam Khamenei ya bayar da rahoton cewa, a kalla matukan jirgi 16 na sojojin gwamnatin sahyoniyawan ne aka kashe sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai a yakin kwanaki 12.
Babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin soji Manjo Janar Seyed Yahya Safavi ya bayyana a jiya Litinin game da yakin kwanaki 12 da gwamnatin yahudawan sahyuniya suka yi, inda ya ce kamar yadda Amurka da Isra’ila suka gaza cimma manufarsu a yakin da aka yi musu, su ma ba su yi nasara ba a wannan yakin. A cewar Manjo Janar Safavi, a yayin wannan yakin, Iran ta harba makamai masu linzami sama da 500 zuwa yankunan da ta mamaye, lamarin da ya haifar da barna mai yawa ga cibiyoyin Isra’ila a Haifa da sauran yankuna.
Manjo Janar Safavi ya kara da cewa yayin harin makami mai linzami da aka kai kan cibiyar horar da matukan jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan, an kashe matukan jiragen Isra’ila akalla 16. Sai dai gwamnatin mamaya na hana fitar da cikakkun bayanai dangane da barnar da aka yi da kuma asarar da aka yi a yakin na kwanaki 12.