Kwamandan dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya yi rangadi a sananonin sojin ruwa na kasa Iran da ke yankin Gulf, inda ya yi duba shirye-shiryen da suke yi na tunkarar kowace irin barazana daga waje a kan kasar.
Da yake jawabi ga sojojin ruwa na kasar ta Iran a yayin wannan rangadi, kwamandan na IRGC ya bayyana cewa, kamar yadda sojojin ruwa suka taka rawar gani wajen tunkarar shishigi na makiya a lokacin yakin kwanaki 12, har yanzu ma suna a cikin Shirin ko ta kwana domin mayar da martani da dukkan karfinsu a kan duk wani aikin wuc gona iri a kan kasar.
Janar Pakpour ya kuma duba hotuna na jiragen Ruwan yaki na Amurka da suke sintiri a cikin tekun Farisa, wanda sojojin Ruwan kasa Iran din suke dauka kai tsaye da wasu na’urori na musamman.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwan zaman dar-dar da Rashin tabbas a yankin, sakamakon barazanar da Isra’ila ke yi na sake shiga wani sabon yaki tare da Iran.
A ranar 2 ga watan Oktoba, ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya tabbatar da cikakken shirin kasar na kare ikonta da al’ummarta a dukkanin fadin iyakokinta.
Nasirzadeh ya bayyana cewa “Iran a shirye take ta kare kasarta ba tare da la’akari da la’akari da duk wani sintiri da kai komo na sojojin makiyanta a cikin tekun farisa ba.