Janar Fadwi wanda shi ne mataimakin kwamndan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya ce; Muna aiki akan nisan Zangon da makamanmu masu linzmai za su iya kai wa gare shi.
Fadwi wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis a wurin taron girmama shahidan rundunar dake kula da kare sararin samaniyar Iran, ya kara da cewa; Babu iyaka ko haddi akan aikin da Iran din take yi a fagen kare sararin samaniyarta da kuma samun karfi.
Dangane da batun da makiya suke yi na rage tsawon Zangon da makamai masu linzami za su ci, Fadwi ya ce; Wasu suna yin Magana akan abinda bai shafe su ba, kuma ba su da wata masaniya akan hakan.”
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Muna yin aiki ne da abinda magabatanmu su ka bamu umarni, kuma babu abinda ya dame su da maganar makiya.
An yi bikin girmama shahid Hassan Tahrani Mukaddam wanda shi ne ya assasa kerewa Iran makamai masu linzami.