Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa
Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba.
Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba.
Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun nan, sun samo asali ne daga matsin lamba na siyasa da nufin tilastawa Iran yin watsi da nasarorin da ta samu.
Ya ci gaba da cewa: Martanin Iran kan duk wani kuduri da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa za ta yi kan Iran zai hada da matakan fasaha, kuma martanin Iran ga hukumar zai hada da sake tantance hadin gwiwar da take bai wa hukumar.
Behrouz Kamalvandi ya yi nuni da cewa: Yayin da nasarorin da Iran ta samu a fannin kimiyya ke ci gaba, za a kara matsin lamba ta siyasa don kawar da kasar daga kan tafarkinta, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba ga wannan matsin lamba.