Iran Ta Yi Allah Wadai Da Furucin Jami’ar Kotun ICJ Na Goyon Bayan Isra’ila

Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa ya mayar da martani ga son zuciya da wata jami’ir kasa da kasa ke

Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa ya mayar da martani ga son zuciya da wata jami’ir kasa da kasa ke yi game da mamayar ‘yan sahayoniyya

Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya yi tsokaci game da kalaman mataimakiyar shugabar kotun kasa da kasa (ICJ) na goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila, yana mai cewa: “Wannan wani lamari ne mai ban mamaki da ya saba wa ka’idojin shari’a da kuma ka’idar rashin son kai na shari’a.”

A wata sanarwa da ya fitar a dandalin X, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da harkokin kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya rubuta cewa: “Wannan wani lamari ne mai ban mamaki da ya saba wa ka’idojin shari’a. Mataimakiyar shugabar kotun kasa da kasa ta fito fili ta bayyana goyon bayanta ga hukumar Isra’ila, yar mamaya a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da shari’a da dama a gaban kotu kan batutuwan matsalolin mamaya da babakere.”

Gharibabadi ya kara da cewa: Wannan ra’ayi na nuna son kai yana zubar da mutuncin kotun kasa da kasa da kuma saba ka’idar amincin shari’a da rashin son kai.

Ya kamata a lura cewa mataimakiyar shugabar kotun kasa da kasa (ICJ) ta Uganda Julia Sebutinde, ta bayyana cewa “Allah yana goyon bayanta, kan tsayawa tare da Isra’ila,” bisa la’akari da cewa “wannan alamun ƙarshen duniya ne da ya bayyana a Gabas ta Tsakiya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments