Jami’an tsaron kasar Iraki sun kama wani dan kungiyar Da’esh ko ISIS da ya yi shigar kayan mata a lardin Neinawa
Majiyar tsaron kasar Iraki ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar sun samu nasarar cafke wani dan kungiyar ta’addancin ta Da’esh ko ISIS a gundumar Al-Baaj da ke lardin Neinewa, yayin da yake sanye da kayan mata a daya daga cikin kasuwannin gundumar.
Majiyar ta ce: ’Yan sandan gundumar Al-Baaj sun kama dan kungiyar ISIS din ne Imad Ali Hassoun Al-Zubaidi a kasuwar gundumar, sanye da kayan mata.
Majiyar ta kara da cewa: “An mika wanda ake neman ruwa a jallo ga hukuma domin gudanar da bincike tare da daukar matakan da suka dace kansa.”