Jami’an Tsaron Hukumar Falasdinawa Sun Kashe Yara Biyu Saboda Taimakon Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya

Jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa sun kashe wasu yara biyu a wani hari da suka kai musu a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan Rahotonnin sun bayyana

Jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa sun kashe wasu yara biyu a wani hari da suka kai musu a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan

Rahotonnin sun bayyana cewa: Yara biyu sun mutu ne bayan da jami’an tsaron Hukumar Cin Kwarya-Kwaryar Gashin Kan Falasdinawa (PA) suka bude wuta kan wata mota da ke dauke da mahaifinsu, da yake dan gwagwarmaya a garin Tamoun da ke arewa maso gabashin Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Jami’an tsaron Falasdinawan sun harbi karamar yarinya ‘yar shekaru uku mai suna Samar Samara kuma ta yi shahada ce sakamakon raunukan da ta samu a jiya Lahadi.

Yayin da dan uwanta Ali dan shekara 16, Ali ya yi shahada sakamakon harbinsa a kai, sannan mahaifinsu ya samu raunuka a kafafuwansa kafin jami’an tsaron Falasdinawan suka yi awon gaba da shi.

Gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila dai tana neman dan gwagwarmayar ruwa a jallo don haka jami’an tsaron hukumar Falasdinawa take taimaka mata wajen kama shi. Bayan kisan gillar, matasan garin Tamoun sun gudanar da zanga-zanga da kuma yajin aiki na gama gari.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yankin Gaza ta yi Allah wadai da ta’addancin, tana mai dora alhakin kisan gillar kan Huumar Falasdinawa da kuma laifukan kashe yara kanana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted