Francesca Albanese, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, ta bayyana a cikin wata sanarwa ta X cewa, a yayin da kotun ICJ ta umurci “Isra’ila” da ta dakatar da kai hare-hare a Rafah, “Isra’ila” ta bijirewa umarnin, ta kuma zafafa kai hare-hare a birnin.
Ta kuma bayyana rahotannin daga iyalan da suka makale a Rafah da cewa halin da suke ciki yana da matukar tayar da hankula.
Albanese ta ce “Isra’ila” ba za ta dakatar da ayyukanta ba, sai dai idan kasashen duniya sun tilasta musu yin hakan. Ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su kakaba takunkumi, wanda zai tilasta hana shigo da makamai ga Isra’ila, da kuma dakatar da huldar diplomasiyya da siyasa a dukkanin matakai tare da “Isra’ila” har sai ta daina kai hare-hare kamar yadda kotun duniya ta umarta.
Shi ma a nasa bangaren Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya yi karin haske kan “wahala da ake fuskanta a zirin Gaza sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila, yana mai jaddada cewa koke-koken da kasashen duniya ke yi kan mamayar Rafah abu ne da bai kamata a yi watsi da shi ba.
Da yake bayyana halin da ake ciki a Rafah a matsayin “wani mummunan bala’i da baya misiltuwa, Griffiths ya jaddada cewa abin da Isra’ila ta yi ya zuwa yanzu, ya yi sanadin tilastawa mutane sama da 800,000 gudun hijira zuwa yankunan da ba su da isassun matsuguni, tsaftar muhalli, da tsaftataccen ruwan sha.