Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu.
Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko. Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau.
A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana ruwa guda a ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da Mosco.
A ranar 18 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne a karon farko tun bayan fara yakin Ukraine jami’an diblomasiyyar kasashen biyu suka hadu a birnin Riyad na kasar Saudiya.