Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kan kasar Yemen
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da kai hare-haren da sojojin Amurka suka kai cikin sa’o’i 24 da suka gabata kan yankuna daban-daban na lardin Sana’a, da Sa’ada da Al-Jawf na kasar Yemen, inda suka lalata kayayyakin more rayuwa da kuma muhallin al’ummar kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana hare-haren da sojojin Amurka suke kaiwa Yemen a matsayin cin zarafi ga ‘yancin kan kasar, da kuma keta ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa. Ya jaddada cewa wadannan hare-haren da ke kaiwa kan gidajen jama’a da kuma ababen more rayuwar al’umma, suna daga cikin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.