Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Yin Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Kan Kasar Yemen

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai tashar jiragen ruwa na Hodeidah da sauran ababen more rayuwa na kasar Yemen, yana mai bayyana hakan a matsayin babban laifi da kuma keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa.

A cikin bayaninsa da sanyin safiyar yau Talata, Baqa’i ya yi nuni da cewa: Hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai kan tashar jiragen ruwa, da masana’antu, da kuma wuraren zama a kasar Yemen, ana aiwatar da su ne tare da goyon baya da kuma taimakon Amurka. Ya bayyana wadannan hare-haren a matsayin cin zarafi ga doka da kuma keta ka’idoji Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya dangane da mutunta ‘yancin kai na kasa da kuma iyakokin kasa. Ya kuma yi kira da a hada kai da daukar kwararan matakai na kasa da kasa da kasashen yankin don dakile kashe-kashe da barna da Amurka da yahudawan sahayoniyya suke yi a kasashen musulmi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta hana yaduwar rashin tsaro a yankin ita ce dakatar da kisan kiyashi da laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Gaza da kuma kawo karshen rashin hukunta masu aikata muggan laifukan a yankin.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments