A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar.
Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas.
Sauran yan takarar sun hada da Firaministan kasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya rike wannan mukami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan kusoshin tsohuwar jam’iyya mai mulki ta PDG.
Kimanin mutum miliyan daya ne aka tantance su kada kuri’a a zaben, daga cikin jimilar miliyan biyu da rabi na kasar.
A karfe 06:00 na yamma agogon kasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na yau aka tsara rufe rumfunan zaben.
Za a iya fara sanar da sakamakon zaben daga gobe Lahadi.