Jakadun kasashen Rasha da Iran sunn gudanar da taro a birninn Vienna inda suka tattauna batun shirin makamashin Nukliya na Iran kafin babban taron hukumar makamashin Nukliya ta Duniya wato IAEA a ranar litinin mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa a jiya Laraba ce Jakadan kasar Iran a hukumar makamashin Nukliya ta duniya Muhsin Naziri Asl, ya gana da tare da jakadan kasar Rasha a cibiyoyin MDD da suke Vienna Mikhail Olyonuf inda bangarorin suka yi musayan ra’ayi kan yadda taron hukumar IAEA na ranarn litinin zata kasance.
A taron hukumar na karshe dai an tada maganar bincike don tabbatar da shirin nukliyar kasar Iran tana tafiya dai dai da kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231. Rafael Gorossi a wani rahoton day a fitar ya bayyana cewa a halin yanzu yawan makamashinn uranium wanda kasar Iran ta tara ya wuce abinda yake cikin yarjeniyar nucliya ta JCPOA da ta cimma da kasashen yamma a shekara ta 2015.
IRAN ya kara da cewa JMI ta dauki makin sabawa yarjeniyar ne bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar ta JCPOA shekru biyu bayan kullata, kuma kasashen turai suka kasa cika alkawulan da suka dauka a cikin yarjeniyar.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar ta tage kan cewa matukar sauran kasashen da suke cikin yarjeniyar sun kasa cika bangarensu na alkawulan da suka dauki Iran ba zata taba komawa kan yerjiniyar ba. Sannan a duk sanda suka cika alkawulan da suka dauka iran a shirya take ta koma kan aiki da yarjeniyar.