Jakadan kasar Yemen a Iran ya jaddada cewa: ‘Yan gwagwarmayar Yemen ba za su dakatar da kai hare-hare kan Isra’ila ba har sai an kawo karshen kai hare-hare kan Gaza
Jakadan kasar Yemen a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ibrahim Al-Dailami ya jaddada cewa: ‘Yan gwagwarmayar kasar Yemen ba za su dakatar da ayyukansu a cikin teku kan jiragen ruwa da ke zuwa tashar jiragen ruwa na gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya ko kuma ayyukan da suke yi na kai hare-hare cikin sassan yankunan yahudawan sahayoniyya ba, har sai gwamnatin mamayar Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare a kan Zirin Gaza da kuma daga matakin killace yankin na Gaza da aka yin a zalunci.
Al-Dailami ya jaddada a cikin shirin “Daga Tehran” na tashar talabijin na Al-Alam cewa: Tun bayan kaddamar da harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsa, kasar Yemen ta bayyana matsayinta na goyon bayan wannan hari na daukan fansa da kuma tallafawa Zirin Gaza kan hare-haren da yake fuskanta daga yahudawan sahayoniyya, sannan kuma sakamakon killace al’ummar Falastinu, ya zama wajibi a kan sojojin Yemen da wadanda ke goya musu baya na al’ummar Yemen, a kullum mako suke gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da ake zalunta, kuma ya zama dole ga sojojin Yemen musamman rundunar sojin ruwa su gudanar da duk abin da za su iya wajen takurawa yahudawan sahayoniyya da masu goya musu baya wajen hana su zirga-zirga a teku musamman isar da makamai ga ‘yan ta’addan sahayoniyya.