Amurka ta gindaya sharudda ga sabuwar gwamnatin Siriya kafin tallafa mata don samu damar gudanar da shugabanci a kasar
Jakadan Iran a kasar Lebanon Mojtaba Amani ya rubuta wani sako a dandalin “X” da a ciki ya tabo batun sharuddan da Amurka ta gindaya wa sabuwar gwamnatin Siriya kafin samun goyon bayanta.
A cikin sakon nasa, Amani ya bayyana wasu daga cikin sharuddan da Amurka ta gindaya kafin goyon bayan sabbin mahukuntan kasar Siriya, inda ya ce: Bayan ganawar da wakilin Amurka ya yi da Al-Julani jagoran ‘yan adawar da suka kifar dagwamnatin Siriya, Amurka ta bayyana cewa: Dole ne sabuwar gwamnatin Siriya ba za ta bai wa Iran wani matsayi ba domin samun kyakkyawar alaka da gwamnatin kasar ta Siriya.
Amani ya kara da cewa: Shi shaida ne cewa a shekara ta 2011 zuwa 2013 Amurka ta dage kan gindaya irin wannan sharudda ga kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Ihwanul-Muslimina, kuma sun gindaya wa Muhammad Morsi, (Allah Ya yi masa rahama) irin wannan sharudda, kuma bayan sun samu damar ganawa da Morsi shi kadai, sun jaddada masa wannan sharudda amma a lokacin da suka ga ya yi watsi da sharuddan. Sai suka zarge shi da cin amanar Amurka kuma suka goyi bayan abin da ya faru gare shi.