Jakadan Iran A MDD Ya Ce: Akwai Bukatar Gane Irin Wahalhalun Da Iran Ta Sha A Yaki Da Ta’addanci

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne kasashen duniya su gane irin wahalhalun da al’ummar Iran ta sha wajen yaki da

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne kasashen duniya su gane irin wahalhalun da al’ummar Iran ta sha wajen yaki da ta’addanci

Jakadan kasar Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya aike da wasika ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da laifukan da kungiyar ta’addanci ta munafukai {MKO} ta aikata, wanda ya yi sanadin shahadan mutane 23,323, Irawani ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa sun yi furuci da ire-iren wahalhalun da al’ummar Iran suka sha tsawon shekaru da dama da kuma wadanda suka yi shahada a fagen yaki da ta’addanci.

A cikin wannan sakon, Irawani ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta himmatu wajen aiwatar da dokokin kasa da kasa da suka shafi yaki da ta’addanci da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma wajibi ne al’ummar duniya su gane irin wahalhalun da al’ummar Iran suka sha tsawon shekaru da dama a sakamakon yaki da suke yi da ta’addanci.

Ya yi nuni da cewa “ya zama dole a saurari tare da mutunta bukatun iyalan wadanda abin ya shafa, ba tare da nuna siyasar fuska biyu ko kuma yin zarge-zarge marasa tushe ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments