Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce Amurka Tana Da Hannu Dumu-Dumu A Kisan Kiyashin Gaza

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare dangi a Gaza

Jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya yi nuni da ire-iren laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke ci gaba da aikatawa kan al’ummar Falastinu, yana mai bayyana wadannan laifuka a matsayin wani misali karara na kisan kiyashi yana kuma daukar Amurka a matsayin babbar kawa a aikata wadannan muggan laifuka.

A yayin zama na musamman a Majalisar Dinkin Duniya a yammacin jiya Alhamis kan batun boren Falasdinawa “Ankaba” na musamman ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya tana so da cikakken goyon baya da taimakon Amurka ta hanyar kaddamar da harte-haren wuce gona da iri da gangan ta rusa asibitoci, makarantu, kashe mata da yara, kaiwatar da kisan gilla kan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ‘yan jarida da sauransu, lamarin da a halin yanzu ya yi sanadin shahadar mutane kusan 60,000 da jikkata wasu da kuma bacewar wasu da dama.

Babban jami’in diflomasiyyar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Munanan laifukan da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta aikata, ba za a iya musantawa ba, kuma kungiyoyin duniya, kotun duniya da sauran hukumomin shari’a na da masaniya kan irin girman wadannan munanan ayyukan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments