Jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya ne ya bayyana hana a wani rubutu da ya yi a shafinsa na hanyar sadarwa ta al’umma.
Mujtaba Amani ya waffala a shafinsa na X cewa:
“Tawagar Amurka da ta gana da Julani , ta kafa wa sabuwar gwamnatin Syria sharadin cewa; kar ta kuskura ta bai wa Iran damar taka kowace irin rawa a cikin Syria,idan har tana son alakarsu ta yi kyau da Amurkan.
Bugu da kari ya ce: Na kasance shaida akan wannan irin nasihar da Amurkan ta kafawa Ikhwanul-Muslimi a tsakanin 2011 zuwa 2013; sun kuma kafawa Muhammadu Mursi Allah ya yi masa rahama, irin wannan sharadin. Da su ka tabbatar da cewa Mursi ya zama shi kadai, ( babu wata kasa mai taimaka masa kamar Iran) sai su ka ci amanarsa kamar yadda su ka saba; abinda ya faru ( juyin mulkin Sisi) ya faru.”