Tom Barrack, jakadan Amurka a turkiya sannan manzonta na musamman a Siriya da Lebanon ya amince da cewa gwamnatin Trump tana son ta hada mutanen kasar Lebanon da sojojin kasar yaki.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Tom Barrack yana fadar haka a wata hirar da yayi da yan jaridu a birnin Abudhabi a yau Talata, ya kara da cewa ya takurawa gwamnatin kasar Lebanon ta kwance damarar kungiyar Hizbullah.
Jakadan ya kara da cewa Hizbullah makiyarmu ce makiyar HKI kuma tana da karfi, amma ba zamu taba bamawa sojojin Lebanon makamai ba, saboda zasu yaki HKI da su. Amma zami iya basu kananan makamai don su yi mutanen kasar wanda kuma suna kungiyar Hizbullah.