Jakadan Amuka Na Musamman A kasar Lebanon Ya amince Da Kwance Damarar Hizbullah Mataki-Mataki

Jakadann Amurka na musamman a kasar Lebanon Tom Barrack ya bayyana cewa ya yarda da matakan da gwamnatin kasar Lebanon take dauka don kwance damarar

Jakadann Amurka na musamman a kasar Lebanon Tom Barrack ya bayyana cewa ya yarda da matakan da gwamnatin kasar Lebanon take dauka don kwance damarar kungiyar Hizbulla ta kasar,

Shafin yanar gizo na Alarabia na kasar Saudiya ya bayyana cewa Barrack ya shaidawa gwamnatin kasar Lebanon kan cewa yana kirin kungiyar Hizbullah da kuma kasar Iran wadanda dukkaninsu mabiya mazhabar shia ne da sun a cewa su yi aiki da gwamnatin kasar don sasantawa.

Kafin haka dai a ranar 7 ga watan Augusta da muke ciki ne gwamnatin kasar Lebanon ta yanke shawarar kwance damarar kungiyar Hizbullah, sannan ta bawa sojojin kasar umurnin wannan aikin. Kuma ta bawa sojojin kan cewa su kammala wannan aikin zuwa watan satumma mai zuwa.

Amma kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa ba zata yi haka ba, ba zata bada ko da guda ne daga cikin makamanta ba. Sannan zata yi yaki da sojojin kasar Lebanon da kuma wadanda zasu taimaka mata har zuwa mutum na karshe da zasu iya bayarwa don kare makamansu.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted