Jagora: Ba Mu Zaton Tattaunawar Iran Da Amurka Za Ta Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya.

A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba.

Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan shawarwarin da kyakykyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata. A ƙarshen tattaunawar ne za a yanke shawarar kudurin da za a dauka, kuma a matakin farko an aiwatar da tattaunawar cikin kyakkyawan mataki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu suna da ra’ayi sosai game da daya bangaren, amma suna da kyakkyawan fata game da kwarewar da suke da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments