Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya amince da bukatar ma’aikatar shari’a na yin afuwa ga wasu fursunoni sannan kuma da rage yawan shekarun wasu na zaman gidan kurkuku.
Yin afuwar ga fursunonin dai ya zo saboda shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta 1404 da kuma karatowar karamar salla ra 1446. Bugu da kari a wannan tsakanin ne ake bikin kafa tsarin jamhuriyar Musulunci na Iran.
Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran Hujjatul-Islam Wal Muslimin Gulam Muhsin Eji ne ya gabatar da bukatar neman afuwar ga fursunonin ta mutane 1526, wanda kuma ya sami amincewar jagoran.
A kowace shekara a lokutan bukukuwan addini da nasa ana yi wa fursunoni masu kananan laufuka afuwa, yayin da ake rage wa wasu tsawon wa’adin zamansu a gidan kurkuku.