Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran zai karbi bakwancin tawagar jami’an kasar da jakadun kasashen musulmi
A cikin sa’o’i masu zuwa ne Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai karbi bakwancin wasu tawagogin jami’an kasar, baya ga wakilai da jakadun kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Wannan taro ya zo ne domin murnar tunawa da zagayowar ranar aiko fiyayyen halitta, Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w) da sakon addinin Musulunci ga dukkan talikai wanda ya yi daidai da yau Talata 28 ga watan Janairu, kuma daidai da ranar 27 ga watan Rajab shekara ta 1446 bayan hijira.