Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Yaki tsakanin gaskiya da karya ba zai taba karewa ba har abada
A yayin da ya karbi tawagar dalibai da sukaziyarce shi domin gabatar masa da ta’aziyyar yuyayin ranar Arba’in ta Imam Husaini jikan manzon Allah {s.a.w} a ranar Laraba da ta gabata: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Yaki tsakanin rundunar gaskiya irin ta Imam Husaini {a.s}da rundunar karya irin ta Yazidu ba zai taba karewa ba.
Haka nan a jiya Lahadi ma, Jagoran juyin juya halin Musuluncin Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin tawagar dalibai na masu juyayin ranar Arba’in ta Imam Huseini {a.s} a babban dakin taro na Husainiyyar Imam Khumaini (yardan Allah ya tabbatar a gare shi).
A jawabin da ya gabatar ga mahalatta zaman taron, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan wata jumla daga cikin ziyarar Ashura cewa: “Ni mai zaman lafiya ne ga wadanda suke zaman lafiya da ku, kuma ina yaki ga wadanda suke yakar ku,” yana mai fayyace kalmar da cewa: “Yakin da ake yi tsakanin mabiya Imam Husaini {a.s} da magoya bayan Yazidu ba zai taba karewa ba.”
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya kara da cewa: Juyin juya halin Musulunci a Iran ya bude wa matasa wata babbar dama da fage mai fadi, don haka wajibi ne mu yi amfani da wadannan damammaki ta hanyar daukar matakan da suka dace don cimma kyawawan manufofin juyin juya halin Musulunci ta hanyar ingantattun shirye-shirye da kuma samar da ayyuka na tushe na ci gaba da wadata.