Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Karfin kariyar Iran abin alfahari ne ga kawayenta yayin da makiyanta suke kara tsoro
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki wannan batu na kare al’umma da tsaron kasar a matsayin muhimmin abu, ya kuma ce: Karfin tsaron da Iran take da shi shi ne abin da ake magana a kai a yau, kawayen juyin juya halin Iran suna alfahari da shi, yayin da makiyan Iran suke kara shiga cikin tsoro.
A ganawarsa da safiyar yau Alhamis tare da tawagar malamai, kwararru da jami’ai na masana’antar tsaron kasa, Jagoran juyin juya halin ya dauki ranar 22 ga watan Bahman a matsayin biki mai girma da tarihi na al’ummar Iran, yana mai taya al’umma kan zagayowar wannan rana da take matsayin ranar jin kai, yana mai nuni da cewa: Bayan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci, al’ummar Iran suna gudanar da bukukuwan zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasarsu.