Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Hanyar Sayyed Nasrallah za ta ci gaba kuma jininsa ba zai taba tafiya a banza ba
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da wata sanarwa inda a ciki ya mika ta’aziyyarsa ga shahadar babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, yana mai jaddada cewa; Hakika jinin shahidi Sayyid Hasan Nasrallah ba zai tafi a banza ba, kamar yadda zubar da jinin shahidi Sayyid Abbas al-Mousawi bai tafi a banza a gabaninsa ba.
A cikin bayaninsa Sayyid Khamenei ya jaddada cewa: Babban mujahidi, wanda yake dauke da tutar gwagwarmaya a yankin, malamin addini, kuma shugaban siyasa, Sayyed Hasan Nasrallah, ya yi shahada a daren Asabar, ya kuma shiga cikin daula mafi girma.
Sayyid Khamenei ya kara da cewa: Babban malamin gwagwarmaya ya samu ladan sadaukarwa da jihadi na tsawon shekaru da dama da suka gabata domin neman yardan Allah a lokacin yaki mai tsarki.
Sayyid Khamenei ya kuma ci gaba da cewa: Sayyid Nasrallah ya yi shahada ne a lokacin da yake gudanar da shirin kare mutanen yankin Beirut da ba su ji ba ba su gani ba da gidajensu da aka ruguza, kamar yadda ya tsara gudanar da gwagwarmaya tsawon shekaru masu yawa wajen kare al’ummar Falastinu.