Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Gana Da Ministan Cikin Gida Da Gwamnonim Lardunan Iran

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya gana da ministan harkokin cikin gida da kuma gwamnonin Larduna, inda ya basu shawarar amfanin

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya gana da ministan harkokin cikin gida da kuma gwamnonin Larduna, inda ya basu shawarar amfanin da kekyawar yanayin da kasar take ciki don ciyar da kasar Gaba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana cewa, a halin yanzu kasar Iran bata fuskantan watai annoba kamar CoviD19, ko matsalar tsaro a cikin gida da sauran wanda zai hanasu aiki. Ko kuma yake bukatar kudade masu yawa don warwaresu.

Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa kasar Iran a halin yanzu bata fuskantar wata matsala, don haka ya bukaci Gwamnonin lardun su yi amfani da wannan damar don amfani da matasan kasar wadanda suka yi karatu don bukasa tattalin arzikin kasar tare da amfani da dimbin arzikin da All..ya horewa kasar.

Kafin haka dai ministan harkokin cikin gida Eskandar Mumini ya gabatar da jawabi inda yake halin da ake cikin a ayyukan ci gaban da gwamnonin suke yi a duk fadin kasar ya kuma bayyana ire-iren ci gaban da aka samu.

Jagoran a wani wuri ya fadawa gwamnonin kan cewa suna iya amfani da kungiyoyin raya kasashen wadanda Iran take da su don kalla yarjeniyoyi da wadannan kasashen saboda ci  gaban kasar Iran. Yace kungiyoyi kamar shanhai, da ECO da sauran su zasu iya taimakawa don kawo ci gaban tattalin arzikin kasar.

Sannan daga karshe jagoran ya bukaci gwamnanin su rika ciga mutane suka tambayansu matsaloli duk da cewa wani lokacin sukan hadu da wadanda zasu fada masu maganganu marasa dadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments