Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Dole Ne ‘Yan Sahayoniyya Su Fihimci Karfin Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Wajibi ne al’ummar yahudawan sahayoniyya su fahimci irin karfin da al’ummar Iran suke da shi Jagoran juyin

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Wajibi ne al’ummar yahudawan sahayoniyya su fahimci irin karfin da al’ummar Iran suke da shi

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi tsokaci kan muhimmancin tsaro a dukkan al’amuran al’umma da kuma bangarori daban-daban na rayuwar jama’a, yana mai jaddada cewa, Iran mai karfi ce da ita kadai za ta iya samar da tsaro da kuma tabbatar da shi da kuma samar da ci gaba ga al’umma yadda ya dace. Don haka dole ne karfin Iran ya karu kowace rana a dukkan fannonin tattalin arziki, kimiyya, siyasa, tsaro da gudanarwa.

A lokacin da ya karbi bakwancin iyalan shahidai da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare tsaron kasa a yau Lahadi, Imam Khamenei a cikin jawabinsa ya yi ishara da mummunan yunkuri da yahudawan sahayoniyya suka yi a daren Juma’a wayewar garin Asabar, inda ya ce: Sun wuce gona da iri kan abin da ya faru da wasu wurare. amma harin bai yi haifar da hasara mai girma da muhimmanci ba, sannan kuskure ne mai girma.

Jagoran ya jaddada wajabcin dakile kura-kuran da yahudawan sahayoniyya suke son yi kan Iran, ya kuma kara da cewa: Wadannan mutane ba su san irin karfin da al’ummar Iran suke da shi ba, kuma ba za su sani ba, don haka akwai bukatar koya musu darasi a fagen rayuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments