Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wata tawagar kwamandojin sojojin ruwa na kasar Iran, inda ya jaddada wajabcin kara karfin makaman yaki da sojojin kasar suke da shi don dakile duk wasu hare-haren wuce gona da iri da makiya zasu kai kan kasar.
A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar sojojin ruwa na kasar Iran wato ranar 25 ga watan Nuwamba, da kuma zagayowar ranar gwarzon sojojin ruwa na Iran “Pekan” da ya kalubalanci sojojin Baath na Saddam, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya tarbi tawagar kwamandoji da jami’an sojojin ruwa na Iran a yau Laraba.
A yayin zaman taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wadannan dakaru a matsayin runduna masu muhimmanci da kuma yanke hukunci a duniya ta yau, sannan ya yaba da ayyuka daban-daban, na leken asiri, tallafi, gudanar da gine-gine da kirkire-kirkire a cikin sojojin ruwa na Iran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi imanin cewa kara karfin makaman fada yana hana gigin makiya na kai hare-haren wuce gona da iri kan al’umma, don haka ya kamata sojojin kasa musamman na ruwa su mai da hankali wajen kara shiri da karfin makaman kare kai a dukkan ayyuka da tsare-tsarensu.