Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a dauki kwararan matakai don dakatar da laifukan da ake yi a Gaza
A yayin ganawarsa da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif da tawagarsa a yammacin yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da inganci tsakanin kasashen Iran da Pakistan domin dakile laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza.
A farkon taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana matsayin Pakistan na musamman a duniyar Musulunci, inda ya bayyana jin dadinsa da kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Pakistan da Indiya, tare da bayyana fatansa na warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar lumana.
Haka nan kuma ya yi ishara da matsayar da Pakistan ta dauka kan batun Falastinu a cikin wadannan shekaru da suka gabata, yana mai cewa: Duk da cewa a cikin ‘yan shekarun nan a kodayaushe ana fuskantar kalubale ga kasashen musulmi na kulla alaka da yahudawan sahayoniyya, Pakistan ba ta taba samun irin wadannan fitintinu ba.