Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ko shakka babu ci gaba da gwagwarmayar da ake yi a Lebanon da Gaza zai kai ga samun gagarumar nasara
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya kara da jaddada cewa: Ci gaba da gwagwarmayar da ake yi a yau tare da dukkanin karfi a kasashen Lebanon, Gaza da dukkan Falastinu, ko shakka babu za ta kai ga samun gagarumar nasarar fafutukar tabbatar da gaskiya da ‘yanci al’ummu, kamar yadda aka fahimta daga abubuwan da suke faruwa da kuma alkawarin Ubangiji.
A jiya Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin mambobin majalisar kwararrun masu zaban jagora a karshen taronsu na biyu a cikin wannan shekara ta hijira shamsiyya.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A ci gaba da gwagwarmayar tare da dukkanin karfi a kasashen Labanon da Gaza da Falastinu, kuma babu makawa za su kai ga samun nasarar fafutukar tabbatar da gaskiya da ‘yanci, kamar yadda aka fahinta daga bangaren ci gaban da ake samu, da kuma alkawarin Ubangiji.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Shahidi Sayyid Hasan Nasrullah da shahidan gwagwarmaya sun ba wa Musulunci daukaka da karfafa a bangaren gwagwarmaya.