Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa Babu Wata Kyakkyawar Fata A Tattaunawar Iran Da Amurka

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ba su tunanin cewa tattaunawar Iran da Amurka za ta haifar da kyakkyawan sakamako Jagoran juyin juya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Ba su tunanin cewa tattaunawar Iran da Amurka za ta haifar da kyakkyawan sakamako

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Iran ba ta jiran izinin kowa wajen inganta sinadarin Uranium, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da manufofinta. Jagoran ya ce ba su yarda cewa tattaunawar za ta kai ga cimma nasara ba.

A jiya Talata ne aka gudanar da biki a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) na tunawa da shahadar marigayi shugaban kasa Ayatullah Ibrahim Raisi da mukarrabansa. Bikin ya samu halartar Jagoran juyin juya halin Musulunci, da shugabannin bangarori uku na gwamnati, da manyan jami’ai, da taron iyalan shahidai, da kuma bangarori daban-daban na al’umma.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana a wajen wannan biki cewa: Shahidi Ra’isi bai dauki kansa a matsayin wanda ya fi mutane ba; Ya dauki kansa a matsayi daya daga cikin jama’a, kamar sauran jama’a, har ma kasancewarsa karami fiye da sauran mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted