Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Aike Da Sako Ga Al’ummar Iran Bayan Harin Da Iran Ta Fuskanta

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da sako ga al’ummar Iran bayan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar A yammacin jiya ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da sako ga al’ummar Iran bayan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar

A yammacin jiya ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da sakon ta gidan talabijin ga al’ummar Iran bayan harin ta’addanci na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin ga al’ummar Iran cewa: Sojojin Iran za su yi aiki da dukkanin karfinsu, kuma za su mayar da martani kan wannan mugunyar aniya ta ‘yan sahayoniyya kaskantattu marasa tunani da basira.

Jagoran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba za su fita cikin wannan aika-aika ba, kuma wajibi ne al’ummar Iran su tabbatar da cewa ba za a yi sassauci ko sakaci kan hakan ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted