Jagoran juyin juya halin Musulunci: Iran ba ta bukatar dakarun wanzar da zaman lafiya a kowane mataki a yankin
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin mawakan Imam Husaini {a.s} da mawakan tunawa da tarihin kyawawan dabi’un Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka (a.s) a yau jiya Lahadi.
Kamar yadda aka saba a tsawon shekarun baya, ana gudanar da irin wannan taro ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar shugabara Matan Duniya, Fatimah Al-Zahra, diyar fiyayyen halitta, Manzon Allah (s.a.w), wadda ya zo daidai da zagayowar ranar haihuwa wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Sayyid Ruhollah Khumaini (Allah Ya yarda da shi).
A yayin wannan taro, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Shirin da Amurka ke yi na jan akalar kasashe ya dogara ne a kan daya daga cikin abubuwa biyu: Ko dai neman bautar da a kan matakan zalunci ko kuma kunna wutar rikici da hargitsi a tsakaninsu, inda a halin yanzu suka haifar da rikici da hargitsi a kasar Siriya, kuma yanzu suna zaton sun cimma nasara.
Ya kara da cewa: Daya daga cikin jami’an Amurka ya ce a bayan labule: “Duk wanda ya tada rikici a Iran, za su mara masa baya.” Wawaye marasa zurfin tunani sun dauka zasu samu wani kyakkyawar sakamakon mai girma, amma al’ummar Iran za su dauki matakin murkushe duk wanda ya karbi aikin Amurka a wannan fagen.