A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon.
Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon.
Sheikh Qasim dai ya taka rawar a zo a gani wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.