Jagora Ya Yabawa Kamfanoni Masu Zaman Kansu Sabota Ci Gaban Da Suka Samu Duk Tare Matsin Lamban Da Kasar Ke Fuskanta

A wata ganawa da kamfanonin masu samar da kayaki a cikin gida, jagoran juyin juya halin musulinci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yabawa kamfanoni masu

A wata ganawa da kamfanonin masu samar da kayaki a cikin gida, jagoran juyin juya halin musulinci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yabawa kamfanoni masu zaman kansu da kuma sauran wadanda suke kawo ci gaba a kasar, kan kokarin da suke yin a kawo ci gaban kasar, duk tare da takunkuman tattalin arziki da kuma matsin lamba daga cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa akwai bukatar kafafen yada labarai gaba dayansu su ci gaba da tallawa abubuwan da wadannan kamfanonin suka samar don fahintar da mutane ingancin ayyukansu da kuma abubuwan da suke samarwa a kasar.

Jagoran ya bukaci a aiwatar da doka ta 44 wanda ya shafi, kula da kamfanini masu zaman kansu a nan JMI. Yace idan an aiwatar da wannan dokar za’a dauke wa wadannan kamfanoni abubuwan da zasu jadasu ci gaba ko sayar da kayakin da suka samar a kasar.

Jagoran ya bukaci jami’an gwamnati wadanda abin ya shafa su nemi kamfanoni da kuma masu zuba jari daga cikin gida da farko.

Daga karshe sayyid Aliyul Khamina’e ya bukaci a wayar da kan mata kan irin albarkatun da kuma wuraren zuba jarin da kasar Iran take da su don su maida hankalin su inda ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments