Jagora: Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Yanke Alakarsu Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da gwamnatin ‘yan sahayoniyya gaba daya, da ma yanke alakarsu ta siyasa, tare da mayar da ita saniyar ware.

Ya kara da cewa: A yanzu gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta zama gwamnati mafi zama saniyar ware da kuma kyama a duniya, amma dole ne a rufe hanyoyin sadarwa da ita. Wannan wani nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkanin gwamnatoci. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A ra’ayinsa, daya daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi harkokin diflomasiyyar kasashen musulmi shi ne kira ga gwamnatoci da su yanke alakarsu da wannan gwamnati da farko a fagen kasuwanci, sannan a fagen siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments