Jagora: Samuwar Sojojin Amurka, Burtaniya Da Wasu Kasashen Turai, Ne Ke Hana Zaman Lafiaya A Gabas Ta Tsakiya

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa samuwar sojojin kasashen Amurka da Burtaniya da kuma na

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa samuwar sojojin kasashen Amurka da Burtaniya da kuma na wasu kasashen Turai su suka hana zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar hakaa safiyar yau Laraba, a lokacinda yake ganawa da malamai da masana ilmin zamani da kuma daliban wasu jami’o’i a nan Tehran.

Labarin ya kara da cewa jagoran ya bayyana haka ne yan sa’o’i da cilla makamai masu linzami kan HKI.

Ya kuma kara da cewa wadannan kasashen da suka jibge makamansu a yankin da sunan tabbatar da abinda suka kira  zaman lafiya a yankin, su ne sababin tashe tashen hankula da yake-yaken da suke faruwa a halin yanzu.

Jagoran ya kara da cewa idan wadanan kasashe za su tafi su bara yankin za’a sami zaman lafiya. Kuma mutanen yankin za su gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments