Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; sabanin da yake a tsakanin Jamhuriyar musulunci da Amurka na tushe ne, ba wani abu ne na sama-sama ba.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi da dubban dalibai da iyalan shahidai a jajiberin ranar “Fada Da Masu Girman Kai Na Duniya” da shi ne gobe 13 ga watan Aban/1404= 4/11/2025, ya kara da cewa; Ya zama wajibi a ci gaba da raya wannan rana.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya tabo ydda a ranar 4 ga watan Nuwamba 1979 daliban jami’o’in Iran su ka mamaye ofishin jakadancin Amurka dake birnin Tehran saboda ya zama cibiyar kitsa makirce-makirce akan jaririn juyin musulunci.
Jagoran juyin musuluncin ya ce,abinda ya faru a wancan lokacin ya yake fuskar Amurka ta hakika ta girman kai da dagawa,don haka ya zama wajibi a ci gaba da raya wannan rana.
Ayatullah Sayyid Ali khamnei ya kuma bayyana cewa; Kiyayyar Amurka ga al’ummar Iran ta samo asali ne tun daga kifar da gwamnatin Muhammad Musaddiq da Amurka ta yi, a 1953 alhali an zabe ta ne ta hanayar Demokradiyya,kuma tun wancan lokacin har yanzu Amurka ba ta daina gaba da al’ummar Iran ba.
Dangane da bukatar Amurka na yin aiki tare da Irna, jagoran ya ce za a yi nazarin hakan amma ba a nan kusa ba, kuma sai idan Amurkan ta daina taimakon’yan sahayoniya.