Jagora: Makamin Da Zai Nutsar Da Jirgin Dakon Jiragenku Na Ruwa Ya Fi, Jiragenku Karfi

A wani jawabi da jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamne ya yi, a yau Talata ya ce; A kodayaushe abinda shugaban kasar

A wani jawabi da jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamne ya yi, a yau Talata ya ce; A kodayaushe abinda shugaban kasar Amurka yake fada shi ne cewa; Sojojinmu sun fi na kowa karfi a duniya, to amma hatatta sojojin da su ka fi karfi a duniya, ana iya kwantar da su ta yadda ba za su iya mikewa ba.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Suna kuma cewa, mun aiko da jiragen yaki zuwa Iran, to mun ji. Tabbas jiragen dakon jiragen yaki, suna da hatsari, amma abinda ya fi su zama hatsari shi ne makamin da zai iya nitsar da su a cikin ruwa.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a gaban mutanen gundumar Azarbaijan ta Gabas da su ka kai masa Ziyara,  ya kara da cewa; Shugaban kasar Amurka ya fadi cewa a cikin shekaru 47 Amurka ta rasa yadda za ta yi da jamhuriyar musulunci, ya yi wa al’ummar kasarsa wannan Koken. Wannan furuci ne mai kyau, abinda zan fada masa shi ne cewa; Babu yadda za ka yi da jamhuriyar musulunci ta iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted