Jagora: Karfin Al’ummar Musulmi Zai Iya Kawo Karshen Ciwon Daji Na Yahudawan Sahayoniyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Karfin al’ummar musulmi ya isa ya kawar da ciwon daji na yahudawan sahayoniyya Jagoran juyin

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Karfin al’ummar musulmi ya isa ya kawar da ciwon daji na yahudawan sahayoniyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Da al’ummar musulmi za su yi amfani da karfinsu, tabbas za su iya kawar da cutar daji ta yahudawan sahayoniyya.

A yayin jawabinsa, ga tawagar jami’an Iran, jakadun kasashen musulmi, da kungiyoyin jama’a daban-daban, da kuma baki ‘yan kasashen waje da suka halarci taron hadin kan al’ummar musulmi na kasa da kasa karo na 38, Ayatullah Sayyid Khamenei ya jaddada cewa: Matakin farko a yau na hada kan duniyar musulmi wajen tunkarar gungun masu laifi da kungiyoyin ta’addanci shi ne kasashen musulmi sun yanke alakar                                                                                                         tattalin arziki da yahudawan sahayoniyya gaba daya.

Haka nan Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Manzon tsira Annabin rahama Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w) da jikansa Imam Ja’afar Sadiq (a.s), yana mai nuni da cewa, maulidin Manzon Allah (s.a.w) yana wakiltar cewa karshen Annabawa ya zo da kuma cikakkiyar farin cikin ɗan adam, yana mai jaddada cewa: Annabawan Allah su ne jagororin ayari na tafiyar ɗan adam a tsawon tarihi, sune masu shiryawa zuwa ga hanya madaidaiciya, kamar yadda suke bai wa dan Adam ikon iya tantance hanya ta hanyar fadakar da fitira da karfin tunani da hikima.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments